Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

13 Satumba 2022

08:14:49
1305453

Tunawa Da Ranar Da Aka Fara Kama Shaikh Zakzaky

12 Ga Satumba 1996, Ranar Da Aka Fara Kama Shaikh Zakzaky

A jiya ne 21 ga watan Shahrivar yi yi daidai da 12 ga watan Satumba, a karon farko ake tunawa da ranar da a kama Sheikh Ibrahim Zakzaky, babban shugaban Harkar Musulunci a Nijeriya, wanda jami’an gwamnatin wancan lokacin suka kama shi, tare da kai shi gidan yari.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya ruwaito cewa a karon farko a ranar 12 ga Satumba, 1996, Dakarun soji da jami’an gwamnati suka dira kan Sheikh Ibrahim Zakzaky, Shugaban Harkar Musulunci a Najeriya a gidansa da ke Zariya a Jihar Kaduna ba tare da wani dalili ba kawai dai sun anbaci wasu dalilai na karya kamar gurbata kwakwalan jama’a da daukar mataki Akan tsaron kasa, inda suka kama shi a gaban iyalansa da dalibansa suka kai shi gidan yari.

 

Dr. Ibrahim Al-Mustafa Seminaka, daya daga cikin ‘yan Shi’a kuma wanda ya halarta a unguwar Shaikh Zakzaky a ranar da aka kama shi, ya bayyana sassan wannan labarin kamar haka:

A ranar 12 ga Satumba, 1996, gwamnatin Dagutu a wancan lokacin ta kama Shaikh Zakzaky bisa umarnin Sani Abacha (Sani Abacha Janar ne na sojan Najeriya kuma dan siyasa wanda ya jagoranci shugabancin Najeriya daga 1993 zuwa 1998).

 

Da safiyar ranar ne jami’an ‘yan sanda da sojoji suka far wa gidan Shaikh Zakzaky da makamansu, inda suka yi ta hayaniya ta hanyar yi masa zobe, lamarin da ya sa Shaikh din ya fito daga dakinsa. Daya daga cikin jami’an ya nuna wa Shehin malamin bindigarsa ya nufo shi da takarda a hannunsa ya shaida wa Shehin cewa yana da takardar neman laifin boye makamai da alburusai a gidansa.

 

A martanin da Shehin Malamin ya mayar ya musanta ya ce dan sandan ya amince su shiga gidansa, amma da sharadin dole sai dai mace mace ta yi haka don duba dakunan da ke ciki, sannan ya daga muryarsa ya ce da su: "Matata da iyalina Suna ciki." kuma ba zan bari kowa ya shigo wurin ba”, daga karshe jami’an tsaro sun yi wa gidan binciken kwakwaf amma ba su samu komai ba suka fito.

 

Da sojojin suka fito daga gidan Sheikh sai suka ce masa: Muna rokonka ka taho tare da mu ofishin ‘yan sanda da ke babban birnin jihar Kaduna ka rubuta ka sanya hannu cewa ba a bincike gidanka ba! Da yake mayar da martani, Sheikh ya ce wa dan sandan: Wace irin karya da batanci kake min, a lokacin da ka nuna min takardar binciken ka shiga gidana, yanzu kana neman in ba da shaida a kan wannan lamari?

 

Mukhtar Ibrahim, babban jami’in ‘yan sandan jihar Kaduna, wanda ya rasu kwanan nan, ya waiwaya ga Sheikh, ya ce: “Wannan matakin bai kai na kamawa ba, sai dai kawai don kammala rahoton, za mu kama ka, Nan take sai Shaikh Zakzaky ya ce masa: Kada ka dauka ni wawa ne irinka, ka ce tun farko mun zo kama ka, shi ke nan!

Washegarin da aka kama Shaikh Zakzaky, ‘yan Shi’a da almajiransa sun gudanar da jerin gwano da muzahara a wasu sassan kasar nan, inda jami’an tsaro suka shiga hargitsi, kuma a wannan rana sojoji sun shahadantar da matasa ‘yan Shi’a 13.

 

Bayan haka ne wasu gungun 'yan Shi'a da matasa suka fitar da sanarwa a wasu jaridu da mujallu inda suka sanar da cewa za su fito kan tituna ranar 18 ga watan Satumba, a daidai lokacin da kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, Yakub Shaibu ya sanar da cewa idan mutane sun fito kan tituna to zai zo kan tituna da manyan motoci zai wuce ta kansu kuma zai karya kafafun wadanda aka kama daga baya! To amma duk da wannan barazanar, masu muzaharar a ranar 18 ga watan Satumba sun matsa lamba kan gwamnati da sojoji don kada su sami wata hanya da ba wacce ta wuce a sako Shaikh Zakzaky.

 

Janar Sani Apacha, Janar din sojan da ya yi mulki a matsayin shugaban Najeriya na 10, wasu mutane da ba a san ko su wanene ba ne suka harbe shi a ofishinsa a lokacin da yake zaune a kan kujerar shugaban kasa a ranar 8 ga watan Yunin 1998, lokacin yana da shekaru hudu kacal a kan mulki.