Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

7 Satumba 2022

16:02:39
1304458

​Sojojin Isra’ila Sun Kashe Wani Matashi Musulmi Bafalestine A Yammacin Kogin Jordan

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun harbe wani matashin Bafalasdine har lahira a wani samame da suka kai a sansanin 'yan gudun hijira da ke arewa maso gabashin gabar yammacin gabar kogin Jordan, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankunan da sojojin yahudawan ke ci gaba da kuntata wa al’ummar Falastinu.

A cewar ma'aikatar lafiya ta Falasdinu, Younis Ghassan Tayeh, mai shekaru 21, an kashe shi ne a ranar yau Laraba a sansanin 'yan gudun hijira na Al-Far'a, wanda ke kilomita hudu (mil 2.4) kudu maso yammacin birnin Tubas, bayan da sojojin yahudawa suka harbe shi a zuciya.

Bayanin ya kara da cewa likitocin Falasdinu sun garzaya da matashin zuwa asibiti a Tubas, amma sakamakon samun munan raunuka ya yi shahada ba da jimawa ba.

Sojojin Isra'ila sun kuma kutsa cikin wasu gidaje a wannan sansanin, lamarin da ya haifar da arangama tsakaninsu da Falastinawa mazauna yankin.

Sojojin yahudawan sun yi ta harbe-harbe da harsasai masu rai, da kuma harba da barkonon tsohuwa da kuma gurneti domin tarwatsa masu zanga-zangar.

342/