Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

7 Satumba 2022

16:00:17
1304453

Najeriya Ta Kafa Kwamitin Da Zai Sake Duba Rahoton Briggs Kan Yajin Aikin Asuu

A karo na 13 gwamantin Tarayyar Najeriya ta sanar da sake kafa wani kwamitin da zai yi nazari kan rahoton da kwamitin da Birggs ya gabtar kan tattaunawarsa da kunsgiyar malaman Jami’o’I ta kasa Asuu sakamkon yajin aiki da suke tsunduma na rashin biyansu bukatun da suka ce an kulla yarjejeniya a kansu tsakaninsu da gwamanti tuna shekara ta 2009

Tun da fari dai gwamanti ta kafa wani kwamtin karkashin Nimi Bariggs wani farfasa domin jagoranta mambobin kwamitin domin sake bitar yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kungiyar ta ASUU da kuma kwamitin da aka rusa karkashin jagorancin Jibiril Munzali,bayan da ta zargi gwamanati da yin wasti da dukkan abubuwan da rahoton ya kunsa

Wanna mataki ne ya sanya kungiyar ta ASUU ta yi watsi da tayin da gwamnati ta yi musu kuma ta ci gaba da yajin aiki da ta fara watanni 7 ke nan kuma ta lashi takobin cewa ba za ta koma aiki ba sai an biya dukkan bukatun da aka cimma matsaya akai.

Tun da fari dai ministan ilimi na najeriya Adamu Adamu ya fadi cewa gwamnati ta kara kashi 23.5 ga dukkan ma’aikatan jamioin sai kuma kashi 35 ga manayan malamai wato farfesoshi yace wannan shi ne iya abin da gwamanti za ta iya dauka. Sai dai duk da haka kungiyar ta yi watsi da shi ta bukaci a aiwatar da yarjejejeniyar da aka cimma da kwamitin Birggs ya gabatar.

342/