Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:49:49
1304156

Za A Kashe Dala Biliyan 25 Don Yakar Dumamar Yanayi A Afrika

A jiya Litinin ne manyan kasashen duniya da shuwagabannin kasashen Afrika suka gana a birni Rotterdam don duba irin hanyoyin da za’a bi wajen shawo kan matsalar dumamar yanayi rikice-rikice da ake fama das u a kasahen Afrika.

Manyana kasashen masu karfin tattalin arziki sun sha alwashin yin amfani da kudade da yawansu ya kai dala biliyan 25 nan da shekara ta 2025 don kara fadada kokarin da ake yi wajen shawo kan matsalar dumamar yanayi dake haddasa amabliyar ruwa fari da tsananin zafi a nahiyar

Rabin kudin bankin bunkasa nahiyar Afrika ne da hadin guiwar wakilai daga kasashen Denmark da birtaniya , faransa da kuma netherland suka yi alkawarin bayarwa, haka shi ma Asusun bada lamuni na kasa da kasa da sauran hukumomi sun bada goyon baya wajen kirkiro da wannan shirin.

Nahiyar Afrika na fatan yin amfani da kudaden wajen shawo kan matsalolin da canjin yanayi ke haifarwa kamar fari, ambaliyar ruwa , da kuma kara yawan shuka itatuwa da sauran abubuwan da za su bada kariya da kuma fadada karfin da suke das hi na samar da makamashi da ake sabuntawa.

342/