Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:49:06
1304155

Rasha Da Kawayenta Sun Fara Wani Gagarumin Atisayen Soji

Shugaba Vladimir Putin na Rasha, ya halarci gagarumin atisayen sojin hadakar da ke gudana tsakanin dakarun kasarsa da na China da kuma na wasu kasashe kawayen Moscow a gabashin kasar.

Atisayen wanda kuma ya kunshi dakaru daga India da Syria da kuma Aljeriya zai ci gaba har zuwa gobe Laraba.

Bisa ga alkaluman da Moscow ta bayar dai fiye da sojoji dubu 50 ke atisayen na Vostok-2022 a rukunnan Soji 500.

Atisayen ya kuma hada da manyan kayakin yaki da suka kunshi jiragen sama na yaki da kuma na ruwa.

342/