Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:47:37
1304154

IRGC : Iran Ta Zarce Manyan Kasashen Duniya A Fannin Fasahar Tsaron Sararin Samaniya

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) ya yaba da karfin soja da manyan makamai na kasar, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta zarce manyan kasashen duniya a fannin fasahar tsaron sararin samaniya.

Da yake jawabi a wani biki a ranar Talata, Manjo Janar Hossein Salami ya yaba da gagarumin ci gaban da Iran ta samu a fasahar soji ta zamani da kuma yadda kasar ke dogaro da kanta wajen kera nagartattun kayan aikin soji, duk kuwa da takunkumin da aka sanya mata.

“Muna matsayi na farko a fagen fasaha mai yawa, Hatta a fagen tsaron sama, mun zarce manyan kasashen duniya ta yadda wasu kasashe ke sayen makamanmu,” in ji Salami.

342/