Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:47:11
1304153

Liz Truss Ta Zama Sabuwar Firaministar Biritaniya A Hukumance

Sabuwar firaministar Burtaniya Liz Truss ta kama aiki a hukumance kwana daya bayan zabenta a matsayin shugabar jam'iyyar Conservative.

Tsohuwar ministar harkokin wajen ta Biritaniya, ta gana da Sarauniyar Ingila a fadarta da ke Balmoral Castle da ke Scotland yau Talata a wani bangare na shirye-shiryen rantsar da ita a matsayin firaministar kasar ta gaba.

Wannan na zuwa ne bayan da a safiyar yau din firaminstan mai barin gado Boris Johnson ya gana da Sarauniyar in da ya mika takardar murabus dinsa.

Manyan kalubalen dake gaban sabuwar firaminsitar sun hada da na tattalin arziki a daidai lokacin da matsalar hauhawan farashin kayaki ke dada karuwa a Burtaniya.

Karin dai na da nasaba ne da karuwar farashin makamashi irinsu iskar gas da kuma wutar lantarki dake addabar kasashen turai da dama sakamakon rikicinsu da Rasha kan yakin Ukraine.

342/