Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:46:39
1304152

Iraki: Bangarori Siyasa Sun Amince Yin Aiki Tare

Manyan jagororin siyasa na kasar Iraki, sun cimma matsaya game da komawa teburin sulhu, domin warware rigingimun dake addabar kasar.

An cimma wannan msataya ce yayin zaman da sassan masu ruwa da tsaki a siyasar kasar suka gudanar.

Wata sanarwa da ofishin riko na firaministan kasar Mustafa al-Kadhimi ya fitar, ta ce yayin zaman wanda shugaban kasar Iraki Barham Salih, da kakakin majalissar dokokin kasar, da wakiliyar musamman ta babban magatakardar MDD a kasar, da sauran jiga-jigan jam’iyyun siyasar kasar suka halarta, an amince a kafa wata tawaga mai wakilcin jam’iyyun siyasa daban daban, wadda za ta tsara dabarun gaggauta gudanar da sahihin zabe, da sake nazarin dokar zabe, da sake inganta hukumar zaben kasar.

Har ila yau, sanarwar ta jaddada bukatar yin gyaran fuska ga tsarin siyasar kasar Iraki, ta hanyar kafa dokoki masu alaka, da tsare-tsaren ayyukan hukuma, bisa tanadin kundin tsarin mulki a dukkanin matakai da za a aiwatar.

342/