Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:46:16
1304151

Isra’ila Ta Ce Akwai Yiyuwar Sojinta Ne Suka Bindiga Shireen Abu Akleh

Isra'ila ta ce akwai yiwuwar, sojojinta ne suka kashe 'yar jaridar nan ta tashar Al Jazeera, Shireen Abu Akleh, data rasa ransa sanadin harbin bindiga lokacin da take aiki yayin wani samamen sojojin Isra’ila a yankin Jenin, da ke yammacin yabar kogin Jordan.

Binciken da Isra'ila ta gudanar ya yi ikirarin cewa sojojin Isra'ila sun yi ta luguden wuta a wurin da lamarin ya faru.

Sai dai Isra’ila ta ce ba za ta gudanar da bincike kan laifin da ake zargin sojojinta da aikatawa.

Dama dai tun tuni binciken Majalisar Dinkin Duniya, da na hukumar Falasdinu da kafofin yada labarai da dama da suka hada da CNN da Kamfanonin Dillancin Labarai, ya gano cewa sojin Isra’ila ne suka kashe ‘yar jaridar.

Binciken ya kuma gano cewa babu mayakan Falasdinawa a wurin, kamar yadda Isra’ila ta yi ikirari.

A ranar 11 ga watan Mayu ne sojojin Isra'ila suka bindige Bafalasdiniyar, kuma Ba'amurkiya, Abu Akleh, mai shekaru 51.

342/