Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:44:53
1304148

Rasha Ta Ce Ba Za Ta Sake Bude Bututun Iskar Gas Ga Kasashen Turai Ba Sai Sun Dauke Mata Takunkumai

Gwamnatin kasar Rasha ta bada sanarwan cewa ba za ta sake bude bututun iskar gas mai suna Nord Stream 1 zuwa kasashen Turai ba sai sun dauke mata takunkuman tattalin arzikin da suka dora mata bayan ta shiga yaki a Ukraine.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin fadar shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov, yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa takunkuman tattalin arziki wadanda kungiyar Tarayyar Turau (EU) da Burtaniya da kuma Canada suka dorawa kasar da kuma wasu kamfanonin kasar ne suka sa Rasha ta dakatar da tura iskara gasa cewa kasar Jamus daga St. Petersburg zuwa arewacin kasar Jamus. Kuma matukar ba a cira takunkuman nan ba Rasa ba za ra sake turawa kasashen na Iskar gas ba.

Kakakin fadar Krimlin ya kammala da cewa takunkuman da kasashen yamma suka dorawa kasar Rasha sun hana ta hatta kula da bututun man da ke kaiwa kasashen iskar gas, don haka kada su zargi kowa su zargi kansu.

A halin yanzu dai kasashen turai sun fara neman inda zasu sami isakar gas don dumama gidajensu da kuma aikin kamfanoninsu daga wasu kasashen duniya. For its part, Moscow began to significantly reduce its gas deliveries to Europe through the Nord

342/