Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:43:55
1304146

​ An Halaka Wani Babban Kwamandan Kungiyar ISIS A Garin Dar’a Na Kasar Siriya

Majiyar tsaro a Garin Dara’a na kasar siriya sun sanar cewa dakarun tsaron kasar sun kaddamar da wani hari a garin Dar’a kuma sun yi nasarar Halaka Muhammad Iyad Abdul-Razzaq da ake wa lakabi da Abu Qasim Al-aqrabawi kusa a kungiyar Ta’adda ta ISIS.

Harin da aka kai an rutsa da yan ta’adda ne a maboyarsu ind aka yi ta fafatawa dasu ta hanyar harba musu makamai da bama bamai, kuma ba’a samu wata asara ba a tsakanin sojojin kasar siriya, sai dai wani soja guda daya da aka jiwa Rauni.

Dan ta’adda Alqarbawi ya kasance yana da hannu a hare-hare da aka kai a watannin baya da suka gabata, cike hard a kai harin bomb kan wata motar Bus dake sauke da wasu sojojin kasar Siriya , da kuma yin garkuwa da mutane da kuma kashe wani jami’in yan sanda a ofishin yan sanda na Muzairip

342/