Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:40:53
1304143

IRGC Ya Kaddamar Da Jirgin Ruwan Yaki Wanda Aka Bashi Suna ‘Shahid Sulaimani”

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun kaddamarda sabon jirgin yaki mai sauri kuma wanda yake aiki da tsarin ‘vertical launching system (VLS),’ da kuma sulke na zamani.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ‘Shahid Sulaimani’ jirgin yaki ne mai sauri sosai kuma yana iya cilla makamai masu linzami kan makiya a doron ruwa da kuma karkashin ruwa, wato kan jiragen yakin na Submarine.

Labarin ya kara da cewa a bikin kadamar da sabon jirgin yakin manya –manyan jami’an sojojin kasar da kuma da kuma jami’an gwamnatin ne suka halarci taron. Daga cikinsu akwai babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Major-General Mohammad Bagheri, babban kwamandan IRGC Major-General Hossein Salami, kwamandan sojojin ruwa na IRGC Rear-Admiral Alireza Tangsiri, gwamnan lardin Hormozgan, wakilin jagora da kuma limamin masallacin jumma’a na Bandar Abbas.

Daga karshe labarin ya kara da cewa jirgin yana da kayakin aiki na zamani wanda zai taimaka masa wajen kai farmaki kan makiya ta sama da kasa a halin tafiya da sauri.

342/