Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

5 Satumba 2022

17:05:01
1303770

​Burtaniya: Liz Truss Ta Zama Shugabar Jam'iyyar Conservative

Sakatariyar harkokin wajen Biritaniya Liz Truss ta zama shugabar jam'iyyar Conservative bayan zabenta a yau Litinin, domin karbar ragamar sabuwar gwamnatin Birtaniya wadda za ta gaji Boris Johnson.

Sakatariyar Harkokin Wajen ta samu kashi 57 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da abokin takararta, tsohon ministan kudi Rishi Sunak, ya samu kashi 43 cikin 100, a cewar sakamakon da Graham Brady, wanda ke da alhakin shirya zaben cikin gida ya sanar.

Daga bisani, Truss ta taya mambobin jam'iyyar Conservative Party murnar zaɓen da aka yi mata da kuma yin godiya, ta kuma zayyana ma'auni na manufofinta da za su rage yawan haraji da kuma bin ƙa'idodin jam'iyyar Conservatives da masu jefa ƙuri'a suka yi zaɓe shekaru biyu da suka wuce.

Har ila yau, ta yi alkawarin samar da mafita ga matsalar makamashi, da rage kudin wutar lantarki, da kuma kula da fannin kiwon lafiya.

A matsayinta na shugabar jam'iyya mafi girma a majalisar dokokin kasar, Truss za ta yi aiki a matsayin firaminista har zuwa babban zabe na gaba, wanda dole ne a gudanar da shi nan da Disamba 2024.

A ranar Talata, za ta yi tattaki don ganawa da Sarauniya Elizabeth ta biyu, domin samun goron gayyatar kafa gwamnati.

Truss mai shekaru 47, ita ce firayim minista ta hudu tun bayan zaben raba gardama na Brexit, kuma mace ta uku da ta rike wannan mukami bayan Margaret Thatcher da Theresa May.

342/