Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

5 Satumba 2022

17:02:36
1303765

​Iraki: Sojojin Kasar Sun Kafa Sansani A Kan Hanyoyin Masu Ziyarar Arba’in

Sojojin kasar Iraki sun kafa sansanoninsu a kan hanyar tafiyar masu ziyarar arba’in a dukkan hanyoyin shiga birnin Karbala.

Kamfanin dillancin labaran farnews na kasar Iran ya bayyana cewa manufar sojojin kasar Iraki itace tabbatar da tsaro da lafiyar miliyoyin masu ziyarar arba’in a Karbala da kuma hanyansu da zuwa da komawa daga can.

Labarin ya kara da cewa runduna ta 110 ta dakarun sa kai na Hashdu Shaabi ma, sun bayyana cewa zasu tabbatar da lafiya da tsaron masu ziyarar arba’in daga ciki da wajen kasar.

A ranar 20 ga watan Safar na shekara ta 1444 ne za’a yi juyayin arba’in na shahadar Imam Husain(s) limami na 3 daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s). wanda yayi dai dai da ranar 17 ga watan Satumba na shekara ta 2022.

Ana saran miliyoyin mutanen kasar Iran ne zasu halarci juyayin arba’in a birnin Karbala a wannan shekara.


342/