Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

5 Satumba 2022

17:00:57
1303761

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Ya Gana Da Wakilan Kungiyar Polisariyo A Aljeriya

Mannzon musamman na Majalisar dinkin duniya a yammacin Sahara Staffan de Mistura ya gana da wakilian kungiyar polisariyo masu fafutukar kafa kasarsu mai cin gashin kai, a yammacin yankin shara dake ciki da dinbin arzikin karkashin kasa wanda kasar Moroko take Ikirarin cewa yana cikin iyakokin kasarta ne

A loakcin ganawar ta su wakilin kungiyar ta polasario a majalisar din duniya Sidi mohammad Omar ya fadi cewa mun yi alkwarin yin adalci da ci gaba da zaman lafiya, wanda muka tabbatar a lokacin yarjejeniyar da ta gabata, kuma muna da kwarin guiwa ci gaba da kare hakkokinmu da babu tattaunawa akansu, ta bin hanyoyin da suka dace,

Haka zalika shi ma wani jami’in diplomasiya na kasar Swedish ya ziyarci sansanin yan gudun hijira kuma yayi Magana da matasa da mata na kungiyar ta Saharawi,

Sakatare janar din kungiyar polasario bangaren mata chaba sini yace mun dauke da sako daga matan Saharawi a yankunan da aka mamaye bayan da suka bukaci wakilan da su ziyarci yankin domin ganema idonsu

342/