Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

5 Satumba 2022

17:00:33
1303760

MDD: Ta Soki Isra’ila Kan Kashe Falasdinawa 4 Da Rusa Gidaje 55 A Cikin Makwanni 2

Rahotanni da hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya ta fitar ya nuna cewa a cikin makwanni biyu Isra’ila ta harbe falasdinawa guda 4 tare da rusa gidajen 55 a yankunan da ta mamaye a gabashin birnin Kudus da gabar yammacin kogin jodan, kana ta jikkata sama da falasdinawa 300 a lokacin rikicin da ya barke tsakani daga 16 ga watan Agusta zuwa 1 ga watan Satumba,

Bafalasdine na baya bayan nan da aka kashe shi ne wanda sojojin Isra’ila suka harbe a ranar 1 ga watran Satumba a garin ramalla a wani samame da suka kai ina duke bincike gida –gida.

Wannan ne ya cika adadin falasdinawa 75 ke nan da sojojin Isra’ila suka kashe daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu, yayin da wasu darurruwa masu yawa kuma suka jikkata ciki hard a mata da yara kanana.

Kungiyoyin kare Hakkin dan Adam sun gabatar da rahotanni masu yawa game da yadda sojojin Isra’la suke amfani da karfi fiye da kima wajen tarwatsa zanga zangar lumana da falasdinawa ke yi a yankun da isra’ila ta mamaye, wanda laifuka ne da ya kamata a gabatar da su a gaban kotun duniya domin isra’ila ta girbi sakamakon zalunci da take yi.

342/