Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Lahadi

4 Satumba 2022

20:08:26
1303430

Ganawar Mahalarta Taron Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya Da Jagora

Cikakken Bayanin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ga Mahalarta Babban Taron Majalissar Ahlul Baiti (a.s) Karo Na Bakwai 03/09/2022

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Bisa Dogaro Koyarwar Ahlul Baiti (AS) Ta Hana Cikar Manufofin Masu Girman Kan Duniya.


Jagoran juyin juya halin Musulunci ya dauki tsayayyen tsarin Musulunci a matsayin ilhama ne daga Ahlul-baiti, sannan ya kara da cewa: wadannan taurari masu haskawa da iliminsu na mahanga da kuma hanyoyin aiki da sun koya mana yadda ake bin tafarkin Musulunci abin so ta hanyar da tunani da aiki da Alqur'ani.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti-Abna cewa, a safiyar jiya (Asabar) a wata ganawa da ya yi da mambobin majalisar Ahlul-baiti ta duniya da kuma baki da suka halarci taron majalissar karo na bakwai na wannan majalissar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana girma da soyayyar Ahlul Baiti a duniyar Musulunci ba yada tamka. Kuma ya jadda cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana a matsayin mai dauke da tutar Ahlulbaiti da take adawa da tsarin mulkin danniya, wacce tai imani da cewa babu wani shatancin tafarki da ke tsakanin mazhabobi da kabilanci da kungiyoyi a duniyar Musulunci wanda ya zamo na hakika ne,kawai abunda yake na gaskiya shi ne shatanci tsakanin duniyar Musulunci da bangaren kafirci da girman kan duniya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi umarni mai karfi ga majalisar Ahlul-baiti ta duniya da su yi amfani da daukaka da farin jinin da Ahlul-baiti suke da shi a duniyar musulmi, yana mai cewa: Kamata ya yi majalissar ta zama tushe da zaburarwa ga dukkan musulmi da masu ruhin sha'awar karantarwar Ahlul Baiti na duniya gaba daya da kuma yin aiki ta yadda ya zama hakan abin ado ne ga Ahlul Baiti.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira ilimomi da sanin Ahlul Baiti a matsayin cikakken abu dake kunshe da dukkanin bukatu dai-daiku na bil'adama da kuma al'ummomin bil'adama yana mai cewa: A yau al'ummomin Musulunci suna da matukar bukata ta dukkan bangarori na ilimi na Ahlul-baiti, don haka wajibi ne da ya hau kan majalisar duniya tare da bin ingantattun tsare-tsare masu kyau da kuma amfani da hanyoyin da suka dace da kayan aiki masu inganci, su aiwatar da wannan nauyi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da tsayin dakan tutar jamhuriyar Musulunci a gaban tsarin ma'abuta girman kai, ya kara da cewa: Mabiya Ahlul-baiti da 'yan Shi'a na duniya suna alfahari da cewa tsarin Musulunci ya kare kirjinsa daga dodanni masu kawuna bakwai na tsarin mulkin kama-karya, Kuma tare da tabbatarwar masu girman kai cewa, da yawa daga cikin tsare-tsarensu sun ci tura.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya dauki tsayayyen tsarin Musulunci a matsayin ilhama ne daga Ahlul-baiti, sannan ya kara da cewa: wadannan taurari masu haskawa da iliminsu na mahanga da kuma hanyoyin aiki da sun koya mana yadda ake bin tafarkin Musulunci abin so ta hanyar da tunani da aiki da Alqur'ani.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kira tutar jamhuriyar musulunci ta Musulunci a matsayin tutar adalci da ruhi yana mai cewa: A bayyane yake kuma a dabi'ance duniyar mamaya wacce dukkanin akidarta da ayyukanta suka dogara da abin duniya da kudi da karfi sun tashi da tsayuwa cikin rikici a gaba da wannan tutar.

Ya kira Amurka a matsayin shugaban masu girman kai, ya kuma kara da cewa: Imam mai girma ta hanyar ilahama daga Alkur’ani ya koyawa kowa da kowa su ajiye rabe-raben da ba na hakika ba da ke tsakanin al’ummomin Musulunci tare da kuma yarda da layin rabuwa guda daya kawai, wato shacin da ke tsakanin Musulunci da kafirci da girman kai.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A bisa wannan zurfafan akida cewa goyon bayan Palastinu ya zamo tun daga ranekun farko a cikin ajandar juyin juya halin Musulunci, kuma Imam ya tsaya tsayin daka kan lamarin Palastinu da dukkanin karfinsa, wacce Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana nan har yau bisa ga wannan jumhuriyar siyasa ta Imam Rahel Azim al-Shaan take aiki kuma za ta ci gaba da kasancewa mai tabbatuwa akan a nan gaba.

Ya ce tausayi na musamman da ya ke akwai a tsakanin al'ummomi a duk fadin duniyar musulmi da al'ummar Iran, ya samo asali ne sakamakon riko da al'ummar Iran kan tafarkin Imam, wadda shine watsi da bambancin mazhaba, kungiyancin da kabilanci a duniyar Musulunci. Sannan ya kara da cewa: A kan haka ne a ko da yaushe muke yin muke yin kira ga dukkanin kasashen musulmi, da yin watsi da al'amura kamar su Shi'a da Sunna da Larabawa da wadanda ba na Larabawa ba, da kuma yin aiki da asalin tushe da ka'idoji.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya dauki kwarin guiwar da sauran kasashe ke yi na tsayin daka wajen yaki da cin zarafi a matsayin dalilin yin fushin gwamnatin da kuma kiyayyarsu inda ya ce: kawar da shirin aikata laifukan Amurka a kasashe daban-daban, wanda misali daya daga ciki shi ne kungiyar ISIS, ya haifar da dimbin yawan farfagandar kyamar Iran da Shi'a, da kuma zargin Iran da tsoma baki a wasu kasashe.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta tsoma baki a cikin wasu kasashe, ya kuma kira zargin da mahukunta ke yi na rashin iya hana gagarumin ci gaban da tsarin Musulunci ya samu asalai dsga gazawarsu, ya kuma kara da cewa: Ko shakka babu ya kamata kowa ya yi taka tsantsan da manufofin girman kai, da kada yayi tarayya tare da su.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya lissafo manufofin girman kai a halin yanzu na kara karfafa bambance-bambance da rarrabuwar kawuna a duniyar musulmi inda ya ce: tunzura jama'a da tsara yakin da ake yi tsakanin Shi'a da Sunna, da Larabawa da na wanda ba Larabawa, ko Shi'a da Shi'a, ko Sunna da Sunna wanda a yanzu a wasu kasashe, ana iya ganin siyasar babbar Shaidanwato Amurka, wacce ya kamata atsaya tsayin daka don kiyaye hakan.

Yayin da yake ishara da cewa mabiya Ahlul Baiti su zama tutar hadin kai da kara karfi, ya kara da cewa: Kamar yadda muka fada tun ranar farko na kafa majalisar Ahlul-baiti ta duniya ba yana nufin gaba dada kiyaya da jayyay da wadanda ba Shi’a ba, kuma tun farko mun kasance tare da ‘yan’uwa wadanda ba ‘yan Shi’a ba, wadanda suka tafi a kan tafarki madaidaici.

A yayin da yake mayar da martani ga tambayar "Shin ko akwai wata dabara ta tinkarar rikice-rikicen makiya duniyar Musulunci" Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Ko shakka babu akwai karfin tsayarwa tare da korar girman kai, idan aka yi la'akari da irin karfin hanyar software da na'ura mai kwakwalwa na duniyar Musulunci.

Ya kira da cewa: "Hujjojin gaskiya da koyarwar Musulunci, da dogaro ga Allah, da yin kallon fata ga tarihi, da mas’alar Mahadawiyya" sun a daga cikin iyawar manhajar na’urori na duniyar Musulunci, da kuma yin ishara da matattun gurbatattun tunaninnikan yamma da tsarin dimokuradiyya da tsarin sassaucin ra'ayi. Ya kara da cewa: Tabbas a fagen kera kayan aiki masu girman kai da mulkin mallaka da suke amfani da albarkatun duniyar musulmi da yin amfani da dabaru iri-iri sun karfafa kansu akan hakan, amma karfin dabi'ar da duniyar musulmi take da shi na samun ci gaba yana da girma ta yadda muhimmancinsa. misali guda, wato man fetur da iskar gas, wanda suka kara bayyana ga kowa a yau.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi imani da cewa bunkasuwar karfin iko ya dogara ne da tsayuwar azama, da sanin makiya, da shiriyuwa irin shiriyar Imam mai girma da kuma yin watsi da ayyuka kanana, yana mai cewa: A yau Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin abin koyi da ta ke hakikanin abin koyi a raye. Ta samu dammar ikon nuna juriya wajen fuskantar kowane irin tashin hankali da hare-hare. Tabbas ma'anar zama abin koyi ba wai koyi da tsarin siyasa ba ne, a'a, riko da ka'idoji da tushe na Imami mai daraja.

A karshe ya yi ishara da cewa: makomar duniyar musulmi makoma ce mai haske kuma al'ummar Shi'a za su iya taka rawa a cikinta.

A farkon wannan taro, Ayatullah Ramezani babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti (A.S) ta duniya ya gabatar da rahoto kan zaman taro karo bakwai na wannan majalissar wanda ya gudana tare da halartar manyan mutane daga kasashe 117. Wanda taron akai masa take da "Ahlul Baiti (A.S.) Ne Matattarar Hankali Da Adalci Da Mutunci".

342/