Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Lahadi

4 Satumba 2022

20:06:35
1303429

Sakon Ayatullah Subhani Zuwa Ga Zaman Babban Taron Majalisar Ahlul-Baiti, AS Karo Na Bakwai Na.

Ayatullah Subhani ya fitar da sako ga babban taron majalissar Ahlul-Baiti na duniya karo na bakwai.

Mamfanin dillancin labarai na Ahl-Bait (AS) ya akwo maku rahoton cewa, Ayatullah Jafar Subhani ya fitar da sanarwar ga taron majalisar Ahl-Bait (AS) karo na 7.

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

)إِنَّما یُریدُ اللَّهُ لِیُذهِبَ عَنکُمُ الرِّجسَ أَهلَ البَیتِ وَیُطَهِّرَکُم تَطهیرًا(

Gaisuwa gareku fitattun malamai da manyan mutane na duniyar Musulunci kuma masu kare shi'aMuna girmama magabata a wajen kafa Majalisar Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, a matsayin misali na kyakkyawar kalma wacce tushenta ya kafu, kuma rassanta a sama suke, ga Allah Madaukakin Sarki nake neman ya datar da ku domin ku kara samun nasara a cikin kula da marayu daga cikin iyalan gidan Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, da shiriyarsu ta hankali da shugabancin ruhi.

Ku ne a sahun gaba wajen kare Musulunci tsantsa da mazhabar Shi'a da ake ta zubar da jininta, kuma ku kasance a kan gaba in sha Allahu kuna daya daga cikin mabiya ma'asumai na hakika, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su. Ta wannan hanyar, zan so in jawo hankali ga abubuwa masu mahimmanci:

1. Da farko ina ba da shawarar wajabcin kiyaye hadin kan al'ummar musulmi musamman hadin kan malaman Shi'a, wadanda su ne abin koyi ga dimbin masoya da mabiyan iyalan gidan Annnabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. haka nan wajibcin bin maraji’ai a fagen hukunce hukuncen da suka sahfi siyasa da zamantakewa da rashin rarraba ra’ayoyi a tsakanin malaman Shi'a.

2. Kokarin bayyana shubuhohi da amsa shubuhohin ta hanyar tsarkakakkiyar koyarwar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) da jagoranci da fadakarwa na wadannan ma'abota daraja.

3. Kokarin gane tsirarun 'yan Shi'a a kasashensu don kare hakkinsu na al'umma da ayyukansu na addini.

4. Akwai bukatar malaman Shi'a da su koma kasashensu daga makarantun hauza na Kum da Najaf da sauransu bayan sun kammala karatunsu domin cika umarnin Ubangiji mai girma da gargadi ga al'ummarsu.

5. A yi kokarin rage zaluncin da ake yi wa A’immah da ba su ji ba ba su gani ba, ta hanyar bayyana tsantsar koyarwa da tarbiyyarsu madaukaka, domin babban zaluncinda za a yiwa Imamai shi ne zama cikin rashin sanin wadannan koyarwar ta su, kuma makiya kullum suna kokarin kare mutane da yin nesa da su daga waɗannan koyarwar.

6. Wajabcin kulla alaka tsakanin ‘yan Shi’a da karfafa ma’aikatun iyali bisa ka’ida mai tsanani na bisa ga abunda Ahlul Baiyt Suka koyar, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su.

7. Bukatar bunkasa makarantun Shi'a, fadadawa da karfafa su a adadi da inganci, da kuma fahimtar da dalibai hanyoyin ilmantarwa da wa'azi a sabon zamani.

8. Muhimmancin batun yada koyarwar addini da amfani da sabbin dabaru da sabbin hanyoyi.

A karshe ina tunatar da ku cewa Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce lokacin da ya aika Amirul Muminin zuwa kasar Yaman: ((لَأَنْ یَهْدِیَ اَللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ عَلَی یَدَیْکَ رَجُلاً خَیْرٌ لَکَ مِمَّا طَلَعَتْ عَلَیْهِ اَلشَّمْسُ) Allah ya shiryar da wani mutum ta hannunka yafi maka alkhairi da abunda rana ta hudo akansa, ina fatan kowa da kowa ya zamo silar shiriyar Miliyoyi na mutane zuwa ga Mazhaba dake raya addinin musulunci da koyaarwar makaranatar Ahlal Baiyt (amincin Allah ya tabbata a gare su).

و السلام علیکم و رحمة الله و برکاته 

Jafar Subhani

3 Safar 1444H