Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

4 Satumba 2022

20:00:37
1303425

AU: Ana Samun Kyautatuwar Yanayin Zaman Lafiya Da Tsaro A Afrika

Tarayyar Afrika AU ta ce, ana samun kyautatuwar yanayin tsaro da zaman lafiya a nahiyar, saboda kokari na bai daya da ake yi da zummar rage rikice-rikice a kasashe da shiyoyyin nahiyar.

Shugaban sashen kwance damarar makamai da fasalta bangaren tsaro na AU, Christopher Suna Kayoshe ya shaidawa wani taro a Nairobin Kenya cewa, batun juyin mulki ma, wanda shi ne jigon dake ingiza rashin tsaro ya ragu.

Jami’in ya bayyana yayin taron karawa juna sani na kungiyoyin al’umma da tarayyar AU, kan tsaron Afrika cewa, AU ta matsa kaimi wajen tura jami’an wanzar da zaman lafiya domin tabbatar da kwanciyar hankali a fadin nahiyar.

Ya kara da cewa, akwai kuma kyakkyawan kudurin shugabanci daga shugabannin kasashe mambobin Tarayyar na kawar da rashin tsaro saboda yana zagon kasa ga ajandar ci gaban nahiyar.

Bugu da kari, ya ce AU ta kara karfafa niyyar magance tushen dake sabbaba rashin tsaro a nahiyar.

342/