Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

4 Satumba 2022

19:59:44
1303423

ATMIS, Za Ta Karfafa Ayyukanta Duk Da Hare Haren Al’shabab

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Afrika a kasar Somalia (ATMIS), ta lashi takobin hada hannu da rundunonin tsaron kasar, domin wanzar da tsaro duk da karuwar hare-haren kungiyar al-Shabab a kasar.

Rundunar ATMIS ta yi tir da harin da mayakan kungiyar al-Shabab suka kai a ranar Juma’a da dare kan jerin gwanon motocin ‘yan kasuwa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 20.

Wata sanarwar da runduanr ATMIS ta fitar a Mogadishu, babban birnin kasar, ta jajantawa iyalan wadanda suka rasu, tare da bayyana kudurin ATMIS din na ci gaba da hada hannu da dakarun gwamnatin Somalia wajen wanzar da tsaro da zaman lafiya a kasar.

Mazauna yankin sun bayyanawa masu aiko da rahotanni cewa, harin na baya-bayan nan, na ramuwar gayya ne kan wata kungiyar ‘yan banga ta Ma'awisley wadda ke samun goyon bayan rundunar sojin Somalia, wadda kuma a baya bayan nan ke yakar mayakan al-Shabab da zummar fatattakarsu daga yankin Hiran.

342/