Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

4 Satumba 2022

19:58:58
1303421

Iran: Lokaci Yayi Da Amurka Za ta Yanke Shawarar Da Za ta Tabbatar da Gaskiyarta Kan Yarjejeniyar Nukiliya

Mai bada shawara ga tawagar Iran a tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliya mohammad marandi ya fadi cewa lokaci yayi da Joe Biden shugaban Amurka zai nuna da gaske yake yi a shawarar da zai yanke kan bukatun da Iran ta gabatar, domin idan Amurka ta bada shawarar da ta dace to za’a iya cimma yarjejeniya cikin Sauki

Tun da fari a shekara ta 2015 aka sanya hannu tsakanin iran da sauran kasashen turai wato Amurka birtaniya faransa jamus da china da rasha da kuma kasashen Turai inda ya kunshi sa iran ta rage wasu ayyuka a ma’aikatar nukiliya daura da haka za’a sassauta takunkumin tattalin arzikin da aka kakaba mata

Sai dai a shekara ta 2018 gwamntin Donald Trumph ya fice daga yarjejeniyar tare da sake kakabawa iran sabbin takunkumi da dawo da wadanda aka cire,

A baya-bayan nan iran ta mika amsa ga mai kula da siyasar waje na kungiayr tarayyar turai Joseph Burell na shawarwarin da kasashen turai suka gabatar domin mika shi ga kasar Amurka , kuma tuni Washington ta sanar da karbar shawarwarin kasar iran .

342/