Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

4 Satumba 2022

19:58:11
1303419

Kungiyar Jihadil Islami Ta Zargi Isra’ila Da Kashe Bafalasdine Da Take Tsare Da Shi Da Gangan

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya a Jihadil Islami ta yi tir da laifukan da take tafkawa kan fursunoni falasdinawa da take tsare dasu t ace shahadar da musa Abu Mahameed da isra’ila ke tsare da shi a gidan yari ya nuna irin bakar siyasar Isra’ila na kashe fusrsunoni falasdinawa da take tsare da su sannu a hankali.

Haka zalika yazo acikin bayanin cewa Mahameed ba falasdine dan shekaru 40 da haihuwa dake tsare a gidan yarin Isra’ila ya mutu ne sakamakon rashin bashi cikakkiyar kulawa da lafiyarsa a Asibitin isra’ila. Wanda hakan keta hakkin dan adam ne na ci gaba da rayuwa,

Wannan yana zuwa ne kwana biyu bayan da fursunoni falasdinawa 100 suka fara yajin cin abinci na sai baba ta gani afadin gidajen yarin isra’ila domin nuna rashin amincewa da matakin gallaza musu da Isra’ila ke yi da sunan tsarin tsare fursunoni a hukumance.

Ana ta bangaren kungiyoyin kare hakkin bil adama sun bayyana cewa Isra’ila tana take hakkoki da yancin da yarjejiniyar Janeva ta 4 ta bawa dukkan fursunoni Falasdinawa, don haka tsarin israila na tsare fursunoni ya take hakkin bil adama ne.

342/