Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

4 Satumba 2022

19:57:21
1303417

​Iran: Dakarun IRGC Sun Soma Rawar Daji Na Sojojin Ruwa A Jiya Asabar

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran (IRGC) sun soma atisayen sojojin ruwa a garin Delvar na Lardin Bushar a jiya Asabar, kuma sun yi gargadi ga duk wanda yayi katsalanda a cikin atisayen.

Kamfanin dillancin labaran IP ya bayyana cewa na fara wannan atisayen ne don tunawa da jarumin kasar Iran wanda ya yaki turawan ingila yan mulkin mallaka a yankin shekaru 107 da suka gabata wato Ra’is Ali Delvari.

Mataimakin kwamadan runduna ta biyu da dakarun ruwa na IRGC ya bayyana a lokacin fara atisayen kan cewa wannan atisayen sakon abota ce ga dukkan kasashen yankin Tekun farisa, sannan sakon gargadi ne ga dukkan makiya wadanda suke son ci gaba da mamayar kasashen duniya ko kuma samar da zaman dar-dar a yankin.

Yake sojojin Ruwa na kasar Iran zasu maida martani mai tsanani ga duk wanda yayi korarin katsalanda a cikin atisayen.

Labarin ya kara da cewa rundunoni 300 na sojojin Ruwa na IRGC ne suke cikin wannan atisye mai girma, kuma zasu baje kolin makaman zamanin da suke da su don bayyana irin karfin da suke da shi.

342/