Ana su bangaren mahukumtan kasar Mali sun bayyana cewa ana zargin sojojin kasar Ivory coasat ne na kasancewa sojojin haya, zargin da Ivory coast ta musanta tare da bayyana cewa suna aikin ne karkashin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya.
Mahukumtan kasar Ivory Caost ta yi alkawarin ci gaba da bibiya lamarin na kasar Mali bisa dokokin majalisar dinkin duniya da ya shafi aikewa da dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar,
Mali ta zargi Abidjan da goyon bayan kasashen yamacin Afrika wajen kakaba takunkumi sojojin dake mulki a kasar bayan juyin mulki da aka yi har sau biyu tuna a shekara ta 2020.
342/