Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

4 Satumba 2022

19:56:30
1303415

Iran Ta Ce Shirin Makamanta Masu Linzami Ba Abin Tattaunawa A Kansa Bane

Mai bawa babban kwamandan sojojin kasar Iran shawara kan al-amuran tsaro ya bayyana cewa shirin makamai masu linzami na Jumhuriyar Musulunci ta Irana (JMI) ba abin tattaunawa a kai bane.

Majiyar muryar JMI ta nakalto Amir Khatami yana fadar haka, ya kuma kara da cewa tsarin harkokin tsaro na JMI ya ginu ne kan nuna karfi da tsoratar da makiya JMI ne, don haka babu wani abu da zai sa Iran ta amince da tattauna tsarin tsaron kasar ta wata kasa a duniya.

Khatami ya kara da cewa makiya JMI sun fito da ra’ayin tattauna tsarin makamai masu linzami na JMI bayan da suka ga irin ci gaba mai yawa wanda sojojin Iran suka samu a wannan bangaren.

Ya kuma jaddada cewa JMI zata ci gaba da inganta makamanta a dukkan matakan sojojin kasar don tabbatar da cewa makiya sun sai yi tunani mai zurfi kafin su yi kokarin farwa kasar da yaki.

342/