Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Alhamis

1 Satumba 2022

20:22:06
1302539

Raisi: Mai Da Hankalin Duniya Ga Mazhabar Ahlul-Baiti (AS) Alhakin Ne Da Ke Kan Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya

Shugaban ya ce: Aikin malamai shi ne bayyana maganganun limamai da hanyar ceton bil'adama, kuma idan aka samu ingantaccen fahimtar Ahlul Baiti (a.s) rashin sanin Imam Hussain (a.s.), Amirul Mumineen (a.s.) da Sayyida Zahra (a.s.) da ke damun wannan zamanin zai bayyana karara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahl-Bait (AS) ya kawo rahoton cewa, shugaban kasar Iran Sayyida Ibrahim Raiisy ya bayyana hakan ne a taron Majalisar Ahlul Baiti (AS) Ta Duniya karo na bakwai da aka gudanar a yau Alhamis (01 ga watan September) a zaure taron kolin na birnin Tehran yace: Ahlul Baiti (AS) da kansu sunce ku sanmu don haka sanin da gane Ahlul Baiti (AS) shine nauyi na farko d aya doro akan wanna majalisar ta Ahlul Baiti (AS).


Hujjatul Islam wal-Muslimin Dr. Ibrahim Raisi ya yi la'akari da hanyar ceto al'umma da kuma mutanen wannan zamani don sanin Ahlul Baiti (A.S) ya ce: Ahlul Baiti (A.S) su ne sirrin dukkan alheri da kuma bayyanuwar dukkan abun kyau a sararin samaniya.Dukkan limamai masu tsarki sun kasance suna da matakai guda uku a cikin tsarkakkiyar rayuwarsu; Yarda da matsayin Imamanci da shiryar da mutane, da yaki da zalunci da horar da rayuka masu basira da shiryar da mutane.

Shugaban ya kuma bayyana gagarumin aikin malaman addini shine sanar da limamai da jagororin addini inda ya fayyace cewa: aikin malamai shi ne sanar da maganganun limamai domin shine hanyar ceton bil'adama, kuma idan aka dace da fahimtar Ahlul Baiti (a.s.) ta kafu, ta hakane za a san matsayin sanayyar dan Adam na wannan zamani ga Imam Husaini ya bata.A) da Amirul Muminin (AS) da Sayyidina Zahra (S).

Raisi ya ce: Ahlul-baiti (AS) su ne alamar dukkan alheri da siffar dukkan kyawawan halittun duniya kuma alamar kimiyya, ilimi, da'a, adalci da ruhi ga bil'adama.

Ana cikin kamala rubutawa.....


342/