Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

1 Satumba 2022

20:16:40
1302534

​Najeriya: INEC ta jaddada wa jam’iyyu da ‘yan takara wuraren da ta -haramta yin kamfen

Yayin da ya rage saura wata ɗaya a fara kamfen na zaɓen shugaban ƙasa, na sanatoci da na mambobin majalisar tarayya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyu da ‘yan takara cewa su guji take dokoki, musamman dokokin da hukumar ta haramta a lokacin kamfen.

Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka a cikin wata hira da jaridu a ƙarshen makon da ya gabata. Za a fara kamfen ɗin ranar 28 Ga Satumba, yayin da za a yi zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.

Okoye ya bayyana cewa wuraren da dokar INEC ta hana yin kamfen da tarukan siyasa sun haɗa da coci-coci, masallatai, gine-gine da ofisoshin gwamnatin tarayya ko na jihohi ko ƙananan hukumomi da kuma amfani da mutum-mutumin ‘masquarade’.

Ya ce ya zama wajibi jam’iyyu da ‘yan takara su bi ƙa’idojin da Dokar INEC ta 2022, Sashe na 92 ya gindaya.

Daga cikin sharuɗɗan da Okoye ya jaddada, akwai “yin hani da amfani da mutum-mutumin domin ƙara wa taron siyasa armashi, yin amfani da wuraren ibada, ofisoshin gwamnati ko gine-ginen gwamnati domin yi wa ma’aikata kamfen da sauran su.

“Sashe na 92 na Dokar Zaɓe ta 2022 ya hana rubutawa ko rera taken jam’iyya ko na ɗan takara ɗauke da kalaman zagi, cin fuska ko aibata wani ɓangaren addini, yare, ƙabila ko wani yankin jama’a.

342/