Mista Borrell, ya bayyana hakan ne ranar Laraba, yayin wani taron manema labarai, inda ya yi fatan ganin cikin kwanaki masu zuwa an cimma yarjejeniya a tattaunawar da ake ta neman ceto yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran a 2015.
A halin da ake ciki dai Iran, ta ce tana nazari game da amsoshin karshe da Amurka ta bayar bisa shawarwarin da kungiyar tarayyar turai, ta bayar na ceto yarjejeniyar.
Saidai Iran, ta fake kan cewa tana bukatar tabbaci daga Amurka kan cewa ba zata sake maimaita abunda ya faru a baya ba, inda ta yi fatali da yarjejeniyar tare da sake laftawa Iran jerin takunkumai.