Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

1 Satumba 2022

20:14:54
1302530

Iran Da Rasha Sun Tattauna Kan Batutuwa Da Dama

Kasashen Iran da Rasha, sun kuduri anniyar aiwatar da yarjeniyoyin da suka cimma a tsakaninsu.

Wannan bayanin na kushe ne a sanarwa bayan taron da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka fitar bayan wata ganawa a birnin Moscow jiya Laraba.

Minsitan harkokin wajen kasar ta Iran, ya isa birnin Moscow ne inda ya gana da takwaransa Sergueï Lavrov, a yunkurin aiwatar da yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka sanya wa hannu a kwanakin baya a Ashgabat da kuma Tehran.

Kasashen biyu sun sha alwashin kawo karshen duk wasu matsaloli dake tarnaki ga huldar dake a tsakaninsu domin habaka musaya ta tsakanin kasashen biyu.

Kazalika ministocin harkokin wajen kasashen biyu, sun tattauna kan wasu batutuwan da suka shafi kasa da kasa dama yankin, musamman batun Ukraine, Afganistanm Siriya, Yemen, Iraki, Falasdinu da Caucase ta kudu.

342/