Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

31 Agusta 2022

19:31:17
1302244

Tawagar ‘Yan Majalisar Dokokin Najeriya Na Gudanar Da Ziyarar Aiki A Birnin Tehran

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa Ali Bagheri Kani ya gana da tawagar sada zumunta ta majalisar dokokin Najeriya a birnin Tehran a yau Laraba.

Bagheri Kani ya kuma bukaci tawagar majalisar dokokin Najeriya da ta ziyarci wasu wasu daga cikin domin ganin irin nasarori da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu a fannonin masana'antu, likitanci, kimiyya, fasaha da tsaro.

Ya kara da cewa a cikin shekaru 40 da suka gabata, Iran ta samu gamu gagarumin ci gaba cikin sauri, sakamakon yadda ta mayar da barazana zuwa ga damammaki na dogaro da kai, bisa irin goyon bayan al'ummar kasar suka bayar, da kuma himma da suka yi tukuru wajen ganin sun kai ga wannan buri nasu na ci gaba.

A nasa bangaren, shugaban tawagar sada zumunta ta ‘yan majalisar dokokin Najeriya Salisu Iro Isansi ya bayyana jin dadinsa da ziyarar da suka kai kasar Iran, inda ya yi fatan hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a fagage daban-daban na siyasa da tattalin arziki zai kara fadada yadda ya dace, da kuma cin moriyar hakan tsakanin Iran da Najeriya.

Shugaban tawagar Majalisar ta Najeriya ya kuma yi ishara da ziyarar da ministan man fetur na Najeriya ya kai a birnin Tehran a makon jiya, da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, yana mai bayyana hakan a matsayin wata alama ta azama tsakanin mahukuntan Iran da na Najeriya wajen kyautata alaka tsakanin kasashen biyu a bangarori daban-daban.

342/