Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

31 Agusta 2022

18:47:12
1302234

Ambaliya Ruwa Ta Kashe Mutum 82 A Sassan Nijar

Hukumomi a jamhuriyar Nijar, sun ce mutane 82 ne suka rasa rayukansu kana wasu 102 suka jikkata a ambaliyar da ake fama da ita sakamakon sabkar ruwan sama a wasu sassan kasar tun daga watan Yuni.

Ambaliyar ta kuma raba mutane dubu 118 da 191 da muhalensu tare kuma da hadassa barna mai yawa, a sababin alkaluman da ma’aikatar kula da kare jama’a ta kasar ta fitar a ranar 29 ga watan Agustan nan.

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu 23 sun mutu ne ta hanyar nutsewa a ruwa sai kuma 59 ta ruftawar gini.

Yankunan aka samu hatsarar rayukan sun ne jihohin Marajd dake kudu maso yamma, inda aka samu mutum 32 da suka riga mu gidan gaskia sai kuma 26 a jihar Zinder dake kudu maso gabas.

Larduna 38 matsalar ta shafa a fadin kasar inda godaje 12,570 suka ruguje sai kuma dabobbbi 652 da ambaliyar ta yi awan gaba dasu,.

Bayanai sun ce kasar ta Nijar ta fuskanci ruwan sama masu yawan gaske, kuma ana hasashen nan gaba matsalar ambaliyar ruwan zata iya shafar mutum sama da dubu 350 a tsakanin watan Yuni zuwa Satumba mai shirin kamawa.

342/