Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

31 Agusta 2022

18:44:08
1302229

​Amurka Ta Kirayi Kasar Sin Da Ta Bude Hanyoyin Tuntuba A Tsakaninsu

Fadar White House ta yi kira ga China da ta sake bude hanyoyin tuntuba a tsakaninsu, bayan da ta sanar da dakatar da hakan domin nuna adawa da ziyarar da 'yan siyasar Amurka suka kai a tsibirin Taiwan.

Mai magana da yawun fadar White House Karen-Jean-Pierre ta bayyana a ranar jiya Talata cewa, "Za mu ci gaba da kokarin sake bude hanyoyin tuntuba a tsakaninmu China."

Jean-Pierre ta jaddada cewa, Amurka na da aniyar ci gaba da ba da tallafin soji ga Taiwan, da zurfafa dangantakarta da tsibirin ta hanyar raya harkokin tattalin arziki da cinikayya.

Ta kara da cewa, "Za mu ci gaba da bin manufar "Kasar Sin dunkulalliya guda daya" kuma bisa manufofinmu, jiragenmu na sama za su ci gaba da shawagi a yankin na Taiwan, da kuma zirga-zirgar jiragenmu na ruwa a mashigin Taiwan.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake cikin zaman dardar a yankin Taiwan biyo bayan ziyarar da shugabar majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi da wasu 'yan majalisar dokokin Amurka suka kai tsibirin, da kuma zirga-zirgar jiragen ruwa da jiragen sama na China da na Amurka kusa da tsibirin.

Gwamnatin China dai dai ta bayyana ziyarar ‘yan siyasar na Amurka a Taiwan da cewa da wani mataki ne na tsokana, da ke neman tunzura Taiwan domin ta shelanta ballewa daga kasar China, lamarin da China ta ce za ta fuskance shi da dukkanin karfinta.

342/