Yarjejeniyar nukiliyar da aka rattaba hannu a kai tsakanin iran da sauran kasashen Amurka barktaniya Faransa rasha china Jamusa game da kungiayr EU a shekara ta 2015 iran ta amince ta dakatar da wasu ayyuka da take yi a masana’antarta ta nukiliya ita kuma a sassauta mata takunkumin karyar tattalin arizkin da aka sanya mata.
Sai dai an fara tattaunawar cirewa iran takunkumi zagaye na biyu ne a ranar 4 ga watan Agusta a binrin Vieanna kuma ab gabatar da bukata masu yawa daga bangaren Enriqua Mora mai shiga tsakanin na kungiyar tarayyar turai a tattaunawar ta Vieanna
Dukkan bangarorin Tattaunawar suna kosa a gaggauta cimma matsaya, sai dai hakan zai tabbata ne bisa la’akari da shawarar siyasa da kasar Amurka za ta gabatar kan sauran muhimman batutuwa da suka rage.
342/