Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

29 Agusta 2022

17:35:08
1301662

Iran Da Najeriya Sun Cimma Yarjeniyoyi A Fannin Makamashi

Kasashen Iran da Najeriya, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin samar da makamashi.

Ma’aikatar albarkatun man kasar Iran, ta labarta hakan, tana mai cewa, an kulla yarjejeniyar ne a gaban ministan ma’aikatar albarkatun man Iran Javad Owji, da karamin ministan mai na Najeriya Timipre Sylva.

Da yake tsokaci game da ci gaban, a gefen tattaunawar da suka yi da Mr. Sylva, Javad Owji, ya ce takardun da aka sanyawa hannu na kunshe da tanadin shigar da kwararru, da injiniyoyin Iran zuwa Najeriya, haka kuma kasar za ta rika shigar da sinadarin urea zuwa Najeriyar.

Bugu da kari, Iran ta amince ta yi wa wasu matatun mai na Najeriya kwaskwarima, tare da gina wasu sababbi.

A nasa bangare kuwa, Sylva ya ce Najeriya na fatan amfana daga fasahohin kasar Iran, na cin gajiya daga iskar gas, da gyara, da gina karin matatun mai a kasar, tare da kula da wadanda ke aiki yanzu haka a kasar.

342/