Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

29 Agusta 2022

17:34:01
1301660

​Abdollahian: Iran Na Ci Gaba Yin Nazari Kan Amsoshin Da Amurka Ta Bayar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdollahian tare da Badr Albusaidi, takwaransa na kasar Oman, sun tattauna ta wayar tarho, dangane da ci gaban da aka samu game da tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliya.

A cikin wannan tattaunawar, ministan harkokin wajen kasar Iran yayin da yake yabawa gwamnatin Omani, ya jaddada cewa: Iran tana cikin yin nazarin kan martanin da bangaren Amurka ya bayar, da kuma abin da suka fi mayar da hankali a kansa.

Ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta bayyana ra'ayoyinta bayan kammala yin nazari a kan martanin na Amurka.

Amir Abdullahian ya kara da cewa, manufarmu ta ginu ne a kan cimma yarjejeniya mai kyau, mai karko da kuma kare muradun al’ummarmu.

Ministan harkokin wajen kasar Oman yayin da yake jinjinawa kokarin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take yi da kuma kyakkyawar niyya wajen cimma matsaya, ya bayyana fatansa na ganin cewa tare da hadin gwiwar dukkanin bangarorin za a samu sakamako mai gamsarwa daga shawarwarin da ake yi a Vienna.

342/