Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

29 Agusta 2022

17:33:11
1301658

​Libya: An Sake Yin Artabu Tsakanin Dakarun Dake Gaba A Tripoli

Rahotannin daga birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libya na cewa, da sanyin safiyar yau Litinin wani sabon artabu ya barke tsakanin dakarun da ke da alaka da Firaministan gwamnatin hadin kan kasa ta Libya Abdel Hamid al-Dabaiba, da kuma "Brigade 77" karkashin jagorancin Haitham al-Tajouri.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, fadan ya barke ne a yankin Ain Zara da ke wajen babban birnin kasar Tripoli.

Da sanyin safiyar yau, Dabaiba ya bayyana cewa, an yi arangama da wasu ya kira damasu yunkurin juyin mulki a kan iyakokin Tripoli daga gabashin da kuma yammacinsa.

A daya hannun kuma, gwamnatin Fathi Bashagha da majalisar dokokin kasar Libya ta nada, ta dora alhakin rikicin da ya barke a babban birnin kasar Tripoli, a kan gwamnatin hadin kan kasa karkashin jagorancin Dabaiba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 30 tare da jikkata wasu da dama. rauni.

Ko a daren jiya an yi arangama tsakanin dakarun da ke biyayya ga gwamnatin Bashaga, wadanda suka samu amincewar majalisar a watan Maris din da ya gabata, da kuma wasu masu biyayya ga gwamnatin Dabaiba, wanda ya samu amincewa sakamakon yarjejeniyoyin siyasa da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta, a kokarin da bangarorin biyu suka yi na ganin cewa an gudanar da zabe.

342/