Dos Santos ya yi shugabancin Angola daga 1979 zuwa 2017, ba tare da an zabe shi kai tsaye ba.
Ya rasu ne a ranar 8 ga watan Yuli yana da shekaru 79 a wani asibiti a Barcelona a kasar Spain, inda aka kwantar da shi bayan bugun zuciya.
Mutane da dama ne suka hallara a dandalin Jamhuriyar dake tsakiyar babban birnin kasar a jiya Lahadi.
Daga cikin shugabannin da suka halarci taron har da shugabannin kasashen Portugal da Afirka ta Kudu da Zimbabwe da kuma Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.
A wurin taron, tsohon shugaban kasar Namibia, Sam Nujoma, ya yabawa Dos Santos a matsayin "mai gaskiya kuma mai kishin hadin kan Afirka."
Dos Santos ya kawo karshen yakin basasa a shekara ta 2002 wanda ya kashe mutane 500,000 cikin shekaru 27.
Magoya bayansa suna kallonsa a matsayin "mai son zaman lafiya".
342/