Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

28 Agusta 2022

18:31:48
1301324

Najeriya: Tsohon Tsageran Niger Delta Ya Sami Kontiragin Hana Satar Danyen Mai

Kamfanin NNPC mai kula da al-amuran hakar man fetur da gas a tarayyar Najeriya ya bawa Tompolo tsohon tsageran Naija Delta kuntragin kula da bututan man fetur da suke kudancin kasar don hana sata da kuma fasa bututan mai a yankin.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa Tompolo ya jagoranci wasu tsageru a yankin wajen fasa bututan man fetur da kayakin kamfanin NNPC a yankin a shekara 2000 zuwa sama, har zuwa lokacinda suka sami afawar gwamnatin tarayyar kasar a shekara ta 2016 suka dai aikin barnan da suke yi.

Labarin ya kara da cewa satar man fetur da kuma lalata bututan man sun hana kasar fidda gangan kimani 500,000 a ko wace rana. Wanda yake takaida abinda gwamnatin take fitarwa a ko wace rana zuwa ganga miliyon 1.4.

Kakakin Tompolo ya ce kafinin tsaron nasa zai kula da tsaron dukkan bututan mai fetur na kamfanin a jihohin Bayelsa, Delta, Edo, Ondo da kuma Imo. Hukukumo a wadannan jihohi sun tabbatar da labarin amma sun ce basu san yadda kontragin yake daki-daki ba.

342/