Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

28 Agusta 2022

18:31:06
1301322

Najeriya: Majalisar Dokokin Lagos Ta Bude Bincike Kan Zamban Da Aka Yiwa Mahajjata

Majalisar dokokin jihar Lagos ta bude bincike cikin zamban da aka yiwa mahajjan Hajjin bana na naira miliyon N46. Sannan ma’aikatan hukumar suka raba kudaden a tsakaninsu.

Jaridar Sahara reporters ne ta fallasa labarin a cikin wayan yulin da ya gabata, sannan majalisar ta bude bincike a cikin zargin a ranar Alhamis da suka gabata.

Labarin ya kara da cewa ma’aikatan hukumar mahajjata na Jihar Legos sun karbi Riyal 555 na saudia daga mahajjata 1,672 na hadaya kawai, amma sai aka basu riyal 300 a Saudia wanda ya bar sauran kudade naira miliyon 46 a hannun hukumar.

Daga nan ne wasu jami’an ma’aikatar mahajjatan da wasu jami’an gwamnatin jihar daga ciki har da wani kwamishina suka yi watandar sauran kudaden Mahajjatan na shekara ta 2022 a tsakaninsu.

342/