Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

28 Agusta 2022

18:30:43
1301321

Jamus Tana Duba Yiyuwar Kwace Kamfanin 'Gasprom German' Na Kasar Rasha

Wata jaridar kasar Jamus ta bada labarin cewa gwamnatin kasar tana duba yiyuwar ta maida kamfanin 'Gasprom German' ta kasar Rasha a matsayin ta kasa, don amfanin kanta.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa gwamnatin kasar Jamus ta kwace kamfanin 'Gasprom German' ta kasar Rasha ne bayan da Rasha ta fara ayyukan soje na musamman a kasar Ukraine, daga cikin jerin takunkuman tattalin arzikin da kasashen na Turai suka dorawa kasar.

Bayan haka ne gwamnatin kasar Rasha ta rage yawan isgar gasa da take turawa kamfanin nata na Jamus don amfanin a kasar ta Jamus. Labarin ya kara da cewa idan gwamnatin kasar Jamus ta tsaida shawarar kwace kamfanin 'Gasprom German' zata mika shi ga kamfanin Securing Energy for Europe Holding GmbH (SEEHG) na kasar don ayyukan cikin gida.

342/