Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

28 Agusta 2022

18:29:34
1301318

​Rasha Ta Mika Wa MDD Shaidun Da Ke Tababtar Da Kai Harin Ukraine A Cibiyar Nukiliya Ta ta Zaporozhye

Tawagar Rasha ta dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da shaidun da ke tabbatar da cewa dakarun Ukraine ne suka kai harin bam a tashar nukiliyar Zaporozhye da Rasha ke iko da ita a kudancin Ukraine a ranar 25 ga watan Agusta.

Ofishin na Rasha ya rubuta a shafin Twitter cewa: "Mun rarraba wa mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bayanin da ma'aikatar tsaron Rasha ta shirya wanda ke nuna harin bam da sojojin Ukraine suka kai a tashar nukiliyar Zaporozhye a ranar 25 ga watan Agusta."

Bayan kai harin dai Amurka da kasashen turai a nan take sun zargi Rasha, amma daga bisani kuma bayan da Rasha ta bukaci a tura kwararru na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya zuwa wurin domin gudanar da bincike, da kuma gano wanda ya kai harin, kasashen turai da gwamnatin Ukraine sun noke, sun kuma ki bayar da hadin kai kan hakan.

342/