Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

28 Agusta 2022

18:28:22
1301315

Abdolahian, Ya Kammala Ziyararsa A Nahiyar Afrika

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya kammala ran gadinsa a Afrika, inda ya jadadda karfafa hulda da kasashen nahiyar a matsayin daya daga cikin mayan siyasar waje ta gwamnatin Tehran.

M. Abdollahian, ya kamala ran-gadin ne daga kasar Zanzibar, inda ya gana da shugaban kasar, Hussein Mwinyi, inda suka tattauna kan batutuwa da dama.

Kafin hakan dama ya gana da shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan, inda ya nemi kara karfafa hulda da kasarsa ta fannin kasuwanci, makamashi, masana’antu da kuma fasaha.

A farkon ziyarar tasa babban jami’in diflomatsiyan kasar ta Iran, ya ziyarci kasar Mali inda cen din ma batun karfafa alaka ne ya mamaye ziyarar.

342/