A ranar Juma’a ce shugaban Tunusia Kais Saied, ya tarbi shugaban na ‘yan Polisario, Brahim Ghali, a hukumance a filin jirgin sama, lamarin da bai yi wa masarautar Morocco dadi ba.
Shi dai shugaban ‘yan Polisarion, ya je ne Tunusia domin halartar taron Afrika da Japon.
Saidai bisa ga dukkan alamu tarben da akayi wa shugaban ‘yan POlisarion bai yi wa Moroccon dadi ba, inda ta kira jakadanta tare da fasa halartar taron.
Tunisia wacce ita ma ta janye jakadan nata daga Morocco, ta jadadda cewarsa bata daukan bangarenci game da batun na yankin yammacin sahara kamar yadda dokokin MDD da kungiyar tarayyar Afrika suka tanada a cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar.
Saidai Moroccon ta ce Tunusia ta gayyaci shugaban ‘yan sahrawi din ne a taron bama tare da amincewar Japon ba.