Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

28 Agusta 2022

05:18:44
1301055

Shaikh Zakzaky: Mun Tsaya Kyam A Tafarkin Allah

A jawabin da ya gabatar a ranar Juma’ar karshe ta watan Muharram, Babban Shugaban Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibrahim Zakzaky H, ya yi kira ga mabiya ‘yan Shi’ah su da su tashi tsaye su bi tafarkin Allah.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya ruwaito a ranar Juma'ar karshe ta watan Muharram, Shugaban Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky, a jawabin da ya gabatar, ya bukaci 'yan Shi'a na wannan kasa da su yi tsayin daka da gwagwarmaya don kawar da zalunci da azzalumai domin samun yardar Allah da amincewarsa.

 

A cikin wani gajeren sako da ya fitar a cikin harshen Hausa, ya jaddada cewa: “Muna sane da cewa duniya filin gwaji ne, kuma kasa ce da ake shuka ayyukan alheri da ceto domin nan gobe kiyama, shi ya sa muka tsaya tsayin daka a tafarkin Allah domin samun gamsuwa da yardarsa; Domin mun yi imani cewa Allah Ta’ala shi ne majibinci kuma zai saka mana akan kokarinmu duniya da lahira.