Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

26 Agusta 2022

19:57:49
1300884

Putin Ya Bada Umarnin Karar Yawan Sojojn Rasha

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya rattaba hannu kan wata doka da za ta bayar da damar kara yawan sojojin da kasar ke da su.

Kafofin yada labarai daga Rasha, ce, nan da watan Janairu mai zuwa, kasar za ta samu sama da sojoji mayaka miliyan 2 da suka hada da wasu dakaru na daban sama da miliyan 1.

Matakin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shiga wata na bakwai na rikicin Rashar da Ukraine.


342/