Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

26 Agusta 2022

19:57:01
1300882

Macron Na Ziyarar Farfado Da Alaka Da Kasar Aljeriya

Shugaban kasar faransa Emanuel Macron, ya isa Aljeriya inda ya fara wata ziyara ta kwanaki uku, mai manufar farfado da alakar data tabarbare tsakanin kasashen biyu.

Ziyayar dai ta zo ne a daidai lokacin da Aljeriya, ke bikin zagayowar karshen yakin samarwa da kasar ‘yancin kai a 1962.

Kasuwanci, inganta rayuwar matasa, halin da ake ciki a Mali, makamashin iskar gas na daga cikin batutuwan da zasu mamaye ziyarar.

Dangantaka tsakanin Aljeriya da faransa dai ta yi tsami ne a watan Satumban bara bayan wasu kalamai na shugaba Macron, da kafofin yada labarai suka rawaito inda Macron ya caccaki wata jaridar kasar mai suna Le Monde da ta wallafa labarin cewa Faransar ta yi wa Aljeriyar mulkin mallaka cikin zalunci abin da ya yi wa Aljeriyar zafi.

Tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu ya kai har inda Aljeriya ta janye jakadanta daga Faransa tare da haramtawa jiragen sojin faransa ratsa sararin samaniyarta.

Wanda dai shi ne karo na biyu da Macron, ke ziyara a Aljeriya a matsayinsa na shugaban kasa, bayan wacce ya kai a watan Disamban 2017 lokacin wa’adin mulkinsa na farko.

342/