Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

26 Agusta 2022

19:56:14
1300880

Iran Da Tanzaniya Zasu Hanzarta Fadada Huldar Dake A Tsakaninsu

Kasashen Iran da kuma Tanzaniya, sun sha alwashin hanzarta huldar dake a tsakaninsu ta fannoni da daban-daban.

Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai lokacin da ya isa kasar Tanzaniya ranar Alhamis kasa ta biyu da ya ziyarta a ran gadin da yake a Afrika.

Babban jami’in diflomatsiyyan na Iran, ya ce ’yan kasuwa da masu masana’antu da ke tare da shi a wannan tafiya za su gudanar da wani muhimmin taro a birnin Dar es Salaam domin tattauna hanyoyin da za a inganta dangantakarsu.

A nata bangare ministar harkokin wajen kasar Tanzaniyar, Liberata Mulamula ta yaba da ziyarar da takwaranta na Iran ya kai kasarta, ta kuma shaidawa manema labarai cewa, kasashen biyu na da alaka sosai.

Kafin hakan ministan harkokin wajen na Iran ya ce fadada alaka da kasashen Afirka na daga cikin abubuwan da tsarin diflomasiyya na tattalin arziki na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanya a gaba.

Amir-Abdollahian ya ce, "Tanzaniya na daya daga cikin muhimman kasashe a wannan nahiya ta wannan fanni, wadda a ko da yaushe tana da matsayi na musamman a harkokin wajen Iran, kuma jama'a da jami'an kasashen biyu na da kyakkyawar fahimta a tsakaninsu.

Nan gaba ne ake sa ran ministan harkokin wajen kasar ta Iran, zai karkare ran gadin nasa a Afrika da Zanzibar.

342/