Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

26 Agusta 2022

19:55:16
1300878

Amurka Ta Bada Amsa Ga shawarwarin Da Iran Ta Bayar Na Cire Mata Takunkumi

Kakakin Ma’aikata harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya bayyana a jiya Laraba cewa sun karbi martani da Amurka ta yi kan shawarwarin da kasar Iran ta gabatar da hannun mai shiga tsakanin na kungiyar tarayyar Turai da zai taimawa wajen warware sauran batutuwan da suka rage a lokacin tattaunawar neman cire mata takunkumi .

Yace Iran ta fara yin nazari tare da taka tsantsan kan Amsar da Amurka ta bayar , kuma da sannu za ta mayar da nata martani ga Amsoshin da Amurka ta bayar ta hannu mai shiga tsakanin na kungiyar tarayyar Turai bayan ta kammala nazarin

Tun da farko an sanya hannun kan yarjejeniyar nukiliyar Iran tun ashekara ta 2015 tsakanin Iran da kasahen Faransa Amurka birtaniya jamus Rasha da kasar china da kumar kungiyar tarayyar Turai da iran ta amince da wasu matakai na jingine wasu ayyukan a masana’antar nukiliyarta ita kuma a dauke mata wasu takunkumin karya tattalin arziki da aka sanya mata

Sai dai a shekara ta 2018 tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da yarjejeniyar kuma ya fice daga cikinsa a cewarsa tana cike da kurakurai, kana ya sake kakabawa iran takunkumi da kuma sake sabunta wadana aka cire abaya

342/