Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

26 Agusta 2022

19:54:30
1300876

​Najeriya: Bayan Sakin Fasinjojin Da Ake Tsare Da Su Ne Kawai Za’a Maida Zirga-Zirgan Jiragen Kasa Tsakanin Kaduna Da Abuja

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa ba za ta farfado da zirga-zirgan jiragen kasa tsakanin Abuja da Kaduna ba matukar akwai wani da yake tsare a hannun ‘yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin kasan a ranar 28 ga watan Maris na wannan shekara.

Jaridar Leadership ta Najeriya ta nakalto ministan sifiri Mu’azu sambo yana fadar haka a jiya bayan taron mako-mako wanda shugaban Muhammadu Buhari ya jagoranta a jiya a fadar shugaban kasa.

Sabo ya kara da cewa bai dace mu farfado da zirga-zirgan jiragen kasa tsakanin Kaduna da Abuja a lokacinda iyalan wadanda ‘yan ta’adda suke tsare da su tun bayan harin ba.

Banda haka sambo ya kammala da cewa gwamnatin tarayyar tana fara wani shiri na kara kyautata harkokin tsaro a kan layin dogo tsakanin Kaduna da Abuja, wanda sai ma sai an kammala shi kafin a sake bude hanyar.

A wani labarin kuma hukumar zargi zargin jiragen kasa ta kasa ta bada sanarwan cewa ta yi asarar akalla naira biliyon N3 tun daga ranar 28 ga watan Maris da ya gabata ya zuwa yanzu sanadiyyar harin da aka kaiwa jirgin kasar da yake kan hanyarsa zuwa kaduna.

342/