Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

26 Agusta 2022

19:53:44
1300874

Tunisia Ta Jaddada Matsayinta Na Haramta Duk Wata Haldar Da Isra’ila (HKI)

Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Tunisia ta jaddada matsayin gwamnatin kasar na haramta dukkan huldar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI). Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan kasuwanci na kasar Tunisia yana fadar haka a jiya Laraba.

Ya kuma kara da cewa labaran da wasu kafafen yana labarai suka watsa kan cewa kasar tana huldar kasuwanci da HKI ba gaskiya bane.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin kasar Tunisia tana kan yarjeniyar da aka kulla tsakanin kasashen Larabawa karkashin kungiyar hadakan kasashen, na daina mu’amala da HKI, ko ta wace irice.

Labarin ya kara da cewa, a halin yanzu HKI ta kwace kasar Falasdinu shekaru fiye da 70 da suka gabata, sannan tana aikata mummunan ta’asa kan al-ummar kasar dare da rana a halin da ake ciki.

342/